Lahadi 27 Satumba 2026 - 20:54
Gadon Sayyid Hassan Nasrullah Bayan Shahada; Fina-finai Sun Bayyana Tarihin Rayuwarsa da Gwagwarmayarsa

Hauza/ Wani rahoton nazari da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya fitar ya yi nazari kan gadon da Shahid Sayyid Hassan Nasrullah, tsohon babban sakataren Hizbullah Lebanon, ya bari, tare da duba yadda tsarin zamantakewa da siyasar ƙungiyar Muƙawama ya ci gaba bayan shahadarsa, da kuma shirya fina-finai masu bayani kan ɓangarori daban-daban na rayuwarsa da gwagwarmayarsa.

Rahoton ya bayyana cewa duk da cewa shahadar Sayyid Hassan Nasrullah ta kasance babbar asara ga Hizbullah, tsarin ƙungiyar bai ta'allaka kacokan kan babban sakatarenta ko ƙarfin sojanta ba. A maimakon haka, tana da wata hanyar sadarwa mai ƙarfi ta zamantakewa, siyasa da tattalin arziki, da kuma goyon bayan jama'a, musamman a tsakanin al'ummar Shi'ar Lebanon, waɗanda suka kasance daga cikin muhimman abubuwan da suka taimaka wajen ci gaba da ayyukanta.

A wannan mahanga, rahoton ya yi nuni da wasu nazarce-nazarce daga cibiyoyin bincike na ƙasashen Yamma da Isra'ila, inda ya bayyana cewa hatta a cikin irin waɗannan nazarce-nazarcen, ba a kallon Hizbullah a matsayin wata ƙungiyar soja kawai. A cewar rahoton, gadon Sayyid Hassan Nasrullah ya fi tsarin soja da tsarin jagoranci na ƙungiyar faɗi.

Wani ɓangare na rahoton ya mayar da hankali ne kan fina-finai masu bayani da aka shirya a cikin 'yan shekarun nan game da rayuwa da halayen Sayyid Hassan Nasrullah. Daga cikinsu akwai fim ɗin “Ma'adalat Nasr”, wanda ya ƙunshi sassa biyar, tare da wata doguwar tattaunawa da aka yi da Sayyid Hassan Nasrullah. Fim ɗin ya mayar da hankali kan ɓangarorin siyasa, dabarun jagoranci da tsaro na ayyukansa, da kuma alaƙar da ke tsakaninsa da jagororin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka kuma, fim ɗin “Sham'ul Jam'” ya fi mayar da hankali kan ɓangaren zamantakewar Sayyid Hassan Nasrullah da rawar da ya taka wajen samar da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyi da ƙabilu daban-daban na Lebanon. Masu shirya fim ɗin sun yi ƙoƙarin duba irin salon da ya bi wajen samar da fahimtar juna da haɗin kan al'umma.

Bugu da ƙari, an shirya fim ɗin “Rayuwar Sayyid Hassan Nasrullah”, wanda ya gabatar da labarin rayuwarsa cikin sauƙi, tun daga ƙuruciyarsa da karatunsa har zuwa ayyukansa na siyasa da gwagwarmaya. A gefe guda kuma, fim ɗin “Qalb al-Amin”, wanda mahaifin Sayyid Hassan Nasrullah, Abdulkarim Nasrullah, ya halarta, ya bayyana wasu ɓangarori na rayuwarsa ta sirri, iyalinsa da lokacin ƙuruciyarsa, tare da gabatar da wani sabon hoto na halayen jagoran Muƙawama.

A ƙarshe, waɗannan fina-finai sun yi magana kan rayuwa da gadon Sayyid Hassan Nasrullah daga mahanga daban-daban; tun daga matsayinsa na siyasa da dabarun jagoranci a fagen Muƙawama, zuwa ɓangarorin zamantakewa, iyali da halayensa, lamarin da rahoton ya bayyana a matsayin ci gaba da mayar da hankali kan rayuwarsa da tunaninsa bayan shahadarsa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha